Tsohon shugaban ƙasar Syria, Bashar al-Assad ya bayyana cewa bai yi niyyar ficewa daga ƙasar zuwa Rasha ba – kamar yadda wani bayani da ake tunanin shi ne bayaninsa na farko tun bayan faɗuwar gwamnatinsa, ya nuna.
An sanya bayanin na Assad ne a wata tashar Telegram ta fadar shugaban Syria, a ranar Litinin, duk da cewa babu tabbas kan wane ne ke gudanar da tashar ta Telegram – kuma babu tabbas ko bayanin daga tsohon shugaban ƙasar ne ko a’a.
Bayanin ya ce, sa’ilin da ƴan tawaye keƙoƙarin karɓe iko da babban birnin ƙasar, Assad ya tafi wani sansanin sojin Rasha da ke lardin Latakia “domin ganin yadda lamurra ke tafiya”, amma sai ya iske dakarun Syria sun tsere daga bakin aiki.
Bayanin ya ƙara da cewa a wannan lokacin kuma “an tsananta hari da jirgi maras matuƙi” kan sansanin sojin da ke Hmeimim, daga nan ne Rasha ta yanke shawarar ɗauke shi a jirgi zuwa birnin Moscow.
A cikin sanarwar – wadda aka wallafa cikin harshen Ingilishi da kuma Larabci – tsohon shugaban na Syria ya bayyana abubuwan da suka faru a ranar ta 8 ga watan Disamba – lokacin da aka ƙwace gwamnatinsa – da yadda aka far masa a sansanin sojin na Rasha.
“Kasancewar babu wata tartibiyar hanyar ficewa daga sansanin, Rasha ta buƙaci kwamandojin da ke sansanin su shirya nan take domin kwashe kowa zuwa Moscow da yammacin ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba,” in ji sanarwar.
“Wannan ya faru ne kwana ɗaya bayan ƙwace Damascus, bayan ƙwace duk wasu cibiyoyin soji da hukumomin gwamnati.”
Bayanin ya ƙara da cewa “duk da abubuwan da suka riƙa faruwa ban yi tunanin sauka daga mulki ko kuma tafiya neman mafaka ba, sannan babu wani da ya yi min tayin hakan”.
“A lokacin da ƙasa ta faɗa hannun ta’addanci, babu wata dama ta bayar da gudumawa mai amfani, a lokacin komai bai da amfani,” in ji bayanin.
Babu dai wanda ya ji ɗuriyar Bashar al-Assad sa’ilin da ƴan tawayen ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham suka ƙwace birane da larduna ƙasar ta Syria cikin kwana 12.
A ranar 9 ga watan Disamba, kafafen yaɗa labaru na Rasha suka sanar da cewa an bai wa Assad mafaka a ƙasar – duk da dai babu wata sanarwa a hukumance domin tabbatar da hakan.
Yanzu haka ƴan tawayen na Syria na ci gaba da tattaunawar kafa gwamnati.