Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da naɗin Susan Summerall Wiles, a matsayin shugabar ma’aikatan fadar White House, idan ya karɓi mulki a shekara mai zuwa.
Wata sanarwa da ya fitar ta ce Wiles “ta taimaka mani wajen lashe zaɓe da kafa sabon tarihi a siyasar Amurka, kuma mace ce mai ilimi da ƙwazon aiki wadda ake mutumtawa a duniya baki ɗaya”
“Ina da yaƙinin cewa za ta taimaka mani wajen dawo da martabar Amurka da kuma zama abin koyi”
Kwamitin karɓar mulki na Donald Trump yana aiki yanzu haka domin zaƙulo mutanen da za a naɗa shugabancin manyan sassan gwamnati 15, ciki harda sakataren harkokin waje da kum na tsaro.
Wacece Susie Wiles?
An bayyana Susie Wiles a matsayin ƴar siyasa da ake jin tsoro sosai, kuma wadda ba kowa ne ya santa ba.
Cikin ƙasa da shekjara guda bayan ta shiga harkokin siyasa, Wiles ta samu shiga cikin tawagar yaƙin neman zaɓen Ronald Reagan, gabanin yaƙin zaɓen 1980.
Ta bayar da gagrumar gudunmuwa wajen sauya akalar siyasar jihar Florida.
A 2010, ta tamakawa Rick Scott, wani ɗan kasuwa da bashi da ƙwarewar siysa, wajen zama gwamnan Florida. A yanzu Scott ɗan majalisar dattawa ne.
Wiles ta hadu da Trump ne a wajen zaɓen fitar da gwamni na jam’iyyar Republica a 2015, daga baya kuma ta zama shugabar kwamitin neman zaɓensa a jihar Florida. Ya kuma doke Hillary Clinton a 2016.
Gwamman Florida, Ron DeSantis, wanda ta yi wa yaƙin neman zaɓe ya bayyana ta a matsayin “wadda ta ƙware a gudanar da harkokin siyasa”
Wiles ta yi aiki a kwamitin neman zaɓen Trump, tare da Chris LaCivita, wani fitaccen ɗan siyasar Republican.
Su biyun ne suka tsara yadda Trump ya kai ga nasara a zaɓen da ya gabata.
Wiles mai shekara 67, kaka ce kuma mahaifin ta tsohon ɗan ƙwallo ne kuma ma’aikacin yaɗa labarai, Pat Summerall.
Ta ce ta tashi ne a cikin gidan da ake “matuƙar mutumta al’ada”
Muƙamin shugabar ma’aikatan fadar gwamnati dai babban muƙami ne, kuma da shi ake tsara duk wani mataki na gwamnati.
Masu riƙe da wannan matsayi suna taka gagarumar rawa wajen harkokin yau da kullum a fadar shugaban ƙasa kuma su ne abokan shawarar shugaban ƙasa na farko a kan kowanne mataki da gwamnati za ta ɗauka.